Labarai
Gudanar da aikin jarida bisa ka’ida zai taimaka wa al’umma fahimtar labaran karya- Com. Abbas Ibrahim
Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya NUJ shiyyar Kano, ta bukaci Manema labarai da su ci gaba da gudanar da aikinsu bisa tsarin dokoki da ka’idojin aikin tare da yin la’akari da irin kalu balen da aikin jarida ke fuskanta sakamakon kafafen sada zumunta.
Shugaban kungiyar Kwamared Abbas Ibrahim, ne ya bukaci hakan yayin taron karrama wasu Daraktocin tashar Talabijin ta Abubakar Rimi da kuma kaddamar da iyayen kungiyar da yammacin Alhamis din makon nan.
Kwamared Abbas Ibrahim, ya kara da cewa, ta hakan ne ‘yan jarida za su samu damar gudanar da aiki yadda ya kamata tare da fadakar da mutane yadda za su kare kansu daga labaran karya da ake yadawa da kafafen sada zumunta na zamani.
Shugaban kungiyar ta NUJ shiyyar Kano, ka kuma ce, “Kasancewar a baya-bayan na an yi wa kundin dokokin aikin jarida kwaskwarima, don haka kungiyar za ta fara shirya tarukan kara wa juna sani da gudanar da horon kara kwarewar aiki.”
Shi kuwa shugaban kungiyar ta NUJ reshen Gidan Talabijin din na AR TV, Kwamared Abubakar shehu Kwaru, bayyana makasudin taron da cewa, zai kara karfafa gwiwar wadanda aka karrama din la’akari da irin tarin gudunmwar da suka bayar.
“Muna fuskantar kalubale dangane da samun kudaden shiga, tare da kokarin hada kan mamabobin kungiyar yayin gudanar da wani taro da zai kawo ci gaba musamman ga al’umma,” inji Kwamared Abubakar Kwaru.
A nasa bangaren, guda cikin wadanda aka karrama Malam Ibrahim Kankarofi, ya mika sakon godiya da farin ciki a madadin takwarorinsa.
Malam Ibrahim Kankarofi ya kuma ce, “Muna matukar farin ciki da godiya bisa wannan taro, sannan zai kara mana kaimi wajen gudanar da ayyukan alheri ta yadda ko da ba ka nan za a ce a lokacin su wane aka assasa ko kuma kaddamar da abu kaza.”
Rahoton: Auwal Hassan Fagge
You must be logged in to post a comment Login