Connect with us

Labarai

Jigawa: Mutane 7 sun rasu 53 sun jikkata sakamakon iftila’in guguwa

Published

on

Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 53 suka jikkata sakamakon wata iska mai ƙarfi da ta haddasa barna a ƙananan hukumomi 13 na Jihar Jigawa.

 

Sakataren Zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Hannafi Fagam, ya ce iskar ta shafi gidaje 5,403 a cikin al’ummomi 120.

 

Ya ce mutanen huɗu sun mutu a Dutse, yayin da aka samu mutum ɗaya-ɗaya a Miga, Ringim da Sule-Tankarkar.

 

Haka kuma, iskar ta lalata makarantu sama da 47, asibitoci uku, ofisoshin ‘yan sanda biyu da gidaje da dama.

 

Fagam ya ce gwamnatin jihar ta amince da fitar da kuɗaɗe domin kai agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, tare da ci gaba da tantance irin barnar da aka yi domin raba kayan tallafi cikin gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!