Labaran Kano
Gwamanatin Kano za ta rage yawan baburan adaidaita sahu
Gwamanatin jihar Kano ta bayyana cewa, za ta rage yawan baburan Adaidaita sahu da ke gudanar da sana’ar su a fadin jihar Kano.
Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a yau Litinin, yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala kare kunshin kasafin kudin hukumar a gaban kwamitin kula da ayyuka na majalisar dokokin jihar Kano.
Ya ce, akwai tarin baburan da ke gudanar da ayyukansu a fadin jihar Kano inda hakan ke janyo matsaloli da dama da suka sanya hukumar ba za ta bari a ci gaba da zaman ta ci barkatai game da yadda ake amfani da baburan na Adaidaita Sahu ba ,a jihar Kano.
Haka kuma ya kara da cewa za su sanya wa baburan da suka yi rijista da hukumar na’urar da za ta rika nuna wuraren da baburan ke shiga, kuma ta hakan ne za a rage yawan baburan.
Baffa Babba Dan Agundi, ya kuma ce kamata ya yi a ce baburan Adaidaita sahun da ke gudanar da sufuri ba su wuce 200,000 ba, amma akwai fiye da guda 500,000.