Labarai
Gwamna Abba Kabir ya bukaci sahalewar majalisa don samar da sabbin ma’aikatu 4
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci majalisar dokoki da ta sahale masa domin ya ƙirƙiri sababbin ma’aikatu guda 4 domin ƙara bunƙasa ci gaban jihar.
Gwamnan ya buƙaci hakan ne ta cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar wadda shugabanta Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya karanta yayin zaman zauren na yau Talata.
Ta cikin wasiƙar gwamnan ya bayyana cewa sabbin ma’aikatun da ya ke son samar wa sun haɗa da ta Jin ƙai da yaƙi da talauci da ma’aikatar kula da albarkatun ƙarƙashin ƙasa da ta samar da wutar Lantarki mai zaman kanta ta jihar Kano da kuma ma’aikatan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman.
A nasa ɓangaren, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ya yi ƙarin haske kan wasiƙun da gwamnan ya aike wa majalisar da cewa gwamnan ya dauki matakin ne domin kara kawowa jihar ci gaba mai dorewa musamman ta fuskar tsaro da samar da ababen more rayuwa da sauransu.
Majalisar ta sanya ranar 2 ga watan gobe na Afrilu domin tantance wadanda gwamnan ya tura sunayensu domin naɗa su a matsayin Kwamishinoni kuma wakilai a majalisar zartaswar jiha.
You must be logged in to post a comment Login