Labarai
Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da shirin tura dalibai fiye da 500 karo ilimi

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci bikin kaddamar da tura dalibai 350 zuwa kasashen waje domin ƙaro karatun digiri na biyu, tare da wasu 240 da za su ci gaba da karatu a makarantun cikin gida dake fadin ƙasar nan.
Da ya ke ƙaddamar da tura shirin a dakin taro na Coronation da ke fadar gwamnatin Kano da yammacin ranar Laraba, gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa wannan shiri wani muhimmin bangare ne na manufar gwamnatinsa wajen bunkasa harkar ilimi da habbaka ƙwarewar matasan Kano.
Wasu daga cikin daliban da suka samu damar sun bayyana farin cikin su tare da gode wa gwamnan jihar bisa wannan dama da suka samu.
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi, musamman wajen tura dalibai zuwa manyan jami’o’i na cikin gida da na waje jihar domin kara samu gogewa.
You must be logged in to post a comment Login