Labarai
Gwamna Abba Kabir ya naɗa Hafsat Kutama a matsayin shugabar riƙo ta PCACC

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Barista Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar riƙo ta Hukumar karɓar Korafi da yaƙi da cin Hanci da rashawa ta Jihar Kano.
Naɗin nata dai, ya biyo bayan murabus din da shugaban hukumar Saidu Yahaya, ya yi a yau Talata.
Da safiyar yau ne dai shugaban hukumar ya tabbatar wa Freedom Radio cewa, ya ajiye aikin nasa, ba tare da bayyana wani daliliba.
Rahotonni sun bayyana cewa, sabuwar shugabar rikon Barista Hafsat Kutama ta yi karatun Shariʼa a Jamiʼar Bayero, kuma ta yi aiki da Maʼaikatar Shariʼa ta Kano, kafin daga bisani ta koma aiki a hukumar karbar korafin da Yaki da rashawa, inda gwamnan Kano ya naɗa ta a matsayin sakatariyar hukumar a watan Agustan bara.
You must be logged in to post a comment Login