Labarai
PDP ta sauya dan takararta na gwamnan Kano

Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Kano, Injiniya Bello Gambo Bichi, ya sanar da sauya ɗan takarar jam’iyyar na gwamnan Kano a zaben 2027.
Hakan ya biyo bayan janyewar da Muhammad Bello Dalha ya yi daga takarar, inda kuma jam’iyyar ta maye gurbinsa da Muhammad Sani Abacha, sakamakon masalahar da aka cimma tsakanin ɓangarorin jam’iyyar.
A yayin wani taron manema labarai da jam’iyyar ta gudanar, Muhammad Bello Dalha, ya bayyana cewa, ya janye daga takarar ne bisa radin kansa, bayan an cimma masalaha tare da samun goyon bayan shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi 44 na Kano.
Taron dai, ya samu halartar wakilan hukumar zaɓe INEC, da kuma shugabannin kwamitocin zaɓe na jam’iyyar PDP.
You must be logged in to post a comment Login