Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Badaru ya taya ma’aikatan Jigawa murnar ranar Ma’aikata

Published

on

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, ya taya ma’aikata jihar murnar zagayewar ranar ma’aikata ta bana.

Da ya ke jawabi ya yin taron bikin ranar Ma’aikatan ta bana, gwamnan ya yaba wa ma’aikata bisa yadda suke gudanar da aikinsu domin ci gaban jihar.

Haka kuma gwamnan, ya gode wa ma’aikatan bisa yadda suke karfafa wa gwamnatinsa gwiwa har zuwa wannan matsayi na karshen gwamnatinsa.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya kuma yi alkawarin mika bukatun da kungiyar kwadagon ta gabatar ga sabon gwamnan jihar mai jiran gado don duba yadda za a aiwatar da su.

A nasa bangaren, Shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Jigawa Kwamared Sanusi Alhasaan Maigatari ya yaba wa mambobin kungiyoyin ya yi bisa halartar taron na bana.

Haka kuma, ya mika sakon godiyarsa ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru Abubakar, bisa yadda ta ke bai wa ma’aikata kulawar da ta dace baya ga gina asibitoci da makaranta da sauran wuraren bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!