Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Daliban Sudan sun bukaci gwamnatocin Kano da Jigawa su yi koyi da gwamna El-Rufa’i

Published

on

Kungiyar  dalibai ‘yan Najeriya da ke karatu a kasar Sudan, ta yi kira ga gwamnatocin  juhohin  Kano da Jigawa da kan su yi koyi da gwmanatin jihar Kaduna kan yunkurin da take na dawo da dalibanta da suke karatu a Sudan domin magance musu matsalolin da suke fuskanta.

Dakta Abdulmudallif Ahmad Muhammad wanda mamba ne a kungiyar daliban, kuma Malami a kwalejin nazarin addinin musulunci ta Legal da ke Daura a jihar Katsina, ne ya bukaci hakan, yayin tattaunawarsa da Freedom Radio da safiyar yau, kan halin da daiban Najeriya ke ciki a  kasar  Sudan dama makomar su idan suka dawo gida.

Dakta Abdulmudallif Ahmad Muhammad ya kuma ce, hatta abincin da daliban za su ci, sai iyayansu sun tura musu da kudi ta asusun wani dan kasar Sudan, sannan ya isa gare su don su yi amfani da shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!