Labarai
Gwamna Fintiri ya dakatar da Sarki bisa zargin cin Hanci

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanar da dakatar da Sarkin Daware, Alhaji Hassan Ja’afaru, ba tare da kayyade lokaci ba bisa zarginsa cin hanci da gazawar shugabanci.
Dakatarwar na cikin wasikar da aka sanyawa hannu mai dauke da kwanan watan ranar 25 ga Afrilu wadda Adama Mamman ta sanya wa hannu tare raba ta ga manema labarai.
Ta cikin wasikar an umarci sarkin da ya mika duk kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga sakataren yankin da ya ke jagoranta.
An tuhumi Ja’afaru da laifin kwace gonaki, kin zama cikin masarautar sa da kuma barazana ga zaman lafiya, da Gwamna Fintiri ya ce ba za a kyale wani bangare ba wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin jihar Adamawa, koda na gargajiya ne.
You must be logged in to post a comment Login