Labarai
Gwamna Ganduje ya bukaci hadin kan jam’iyyun adawa
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin sa zata cigaba da bada fifiko wajen samar da tsaro, tare da inganta harkar ilimi da lafiya don ganin jihar ta kai matakin cigaban da sauran kasashen duniya suke da shi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Litinin a dakin taro na Africa House, dake fadar gwamnatin jihar Kano, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan da kotun koli ta tabbatar da shi a matsayin gwamna.
Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce yanke hukuncin ba wai nasararsa bace ko kuma ta wasu mukarrabansa yana mai cewa, “hakan ya nuna cewar nasarar al’ummar jihar Kano ce baki daya da kuma tabbatar da adalcin kotu ga wanda suka shigar da kararrakin zabe”.
Haka kuma gwamnan ya yi kira ga sauran abokan hamayyarsa da suzo su hada kai tare, don cigaban jihar Kano tare da gudanar da manyan aiyyuka don ganin an kammala su tare a wannan tafiyar karo na biyu na gwamnatin sa.
Wakilinmu na fadar gwamnatin jihar Kano Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito cewa dumbin magoya baya da ‘yan siyasa da manyan mukarraban gwamnati ne suka yi dandazo zuwa fadar gwamnatin domin taya gwamnan murnar samun nasarar a kotun koli.