Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Kano Abba Gida-Gida ya taya Ƙasar Najeriya murnar cika shekaru 63 da samun ƴancin kai

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ya taya al’ummar ƙasar nan murnan cikar shekara 63 da samun kai daga turawan mulkin mallaka

Gwamna Abba ya kuma buƙaci shugabanni da suyi koyi da irin gudunmawar da shugaban nin baya suka bayar wajen ciyar da ƙasar nan gaba irin su Malam Aminu Kano, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mallam Sa’adu Zungur, Yusuf Maitama Sule, Chief Anthony Enahoro and Madam Magret Ekpo Sir Ahmadu Bello, Alhaji Sule Gaya, Herbert Macaulay, Dr. Nmandi Azikiwe, Chief Obafemi Awolowo, Hajiya Gambo Sawaba, Madam Funmilayo Ransome-Kuti, Jaja of Opobo and Sir Kashim Ibrahim

Gwamnan yayi wannan jawabin a yau cikin wani ɓangare na cikar ƙasar nan shekara 63 da samun kyancin kai

Gwamna Abba ya kuma ce la’akari da yadda ake tunawa da tsaffin shugabanni wajen ciyar da ƙasar nan gaba ya kamata suma shugabannin yanzu suyi koyi da su.

Ka zalika ya ƙara da cewa ya kamata shugaban ni su tabbatar wa da al’umma cewa sunyi musu abin da suke buƙata domin tabbatar adalci

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!