Labarai
Gwamna Radda ya sha alwashin samar da Ma’aikatar Lantarki

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana shirinsa kafa Ma’aikatar wutar Lantarki, wadda ita ce irinta ta farko a faɗin Najeriya.
Gwamnan ya ce kafa wannan ma’aikata na daga cikin muhimman matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin sauya tsarin amfani da makamashi zuwa wanda ya fi tsafta da araha da kuma ɗorewa.
Radda ya kuma jaddada cewa, sabon tsarin zai taimaka wajen rage dogaro da man fetur, da samar da sabbin hanyoyin samar da haske ga al’umma, musamman a yankunan karkara.
A cewar gwamnan, wannan mataki zai kuma samar da damarmakin ayyukan yi ga matasa, tare da janyo masu zuba jari daga cikin gida da wajen ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login