Kiwon Lafiya
Gwamna Samuel Ortom ya je gaban kwamitin majalisar dattijai kan binciken kashe-kashen jihar sa
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya ziyarci kwamitin majalisar dattijai kan binciken kashe-kashen da ke faruwa a jihar Benue.
A makon da ya gabata ne Kwamitin majalisar Dattawa kan kashe-kashen da ke faruwa a jihar ta Benue, ya gabatar da rahoton sa, inda ya ce babban Sufeton yan sandan kasar nan ya gaza yin abinda ya da ce kan rikicin da ya taso a jihar ta Benue wajen kama wa tare da gurfanar da wadanda ke da hannu cikin rikicin.
Cikin rahoton kuma kwamitin ya bayyana cewa babban Sufeton yan sandan kasar nan ya ce rundunar ta samu nasarar chafke mutane 145 da ke da hannu cikin al’amarin.
Daga nan ne kuma majalisar ta yi watsi da rahoton kwamitin sakamakon rashin jiyo ta bakin gwamnan jihar kan matsalolin tsaro da ke faruwa a jihar, tare da umartar kwamitin da ya koma don jin ta bakin gwamnan kan batun.