Labarai
Gwamna ya dauki nauyin duk kayan saukar da ɗalibai suka yi- Sagagi

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta mayar wa iyayen daliban makarantar Fityatul Qur’anil Murattal, da ke unguwar Dukawuya kudaden da suka kashe na Alluna da Tifafi da sauran kayayyaki da suka kashe na bikin saukar karatun da daliban makarantar fiye da 70 suka yi.
Kwamishinan harkokin kasuwanci jam’iyyun gama kai da zuba jari na Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana hakan yayin bikin saukar karatun a yau Lahadi.
Kwamishina Sagagi, wanda ya kasance mai makarantar da kuma ya dauki nauyin koyar da dalibai karatun Alkur’ani da sauran litattafan addinin Musulunci a kyauta, ya yaba wa malaman makarantar bisa jajircewar su wajen koyar da yaran yadda ya dace.
Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya kuma bayyana farin cikinsa bisa yadda baya ga dalibai 70 suka sauke Alkur’ani mai tsarki akwai kuma dalibai 13 da suke yin karatu duk karshen mako inda suka haddace Izu Talatin a cikin shekara daya.
Kwamishinan Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya kuma sha alwashin ci gaba da daukar nauyin irin wadannan dalibai domin samun ilimi mai inganci.
Ya ƙara da cewa, “Ganin irin wannan abun alkhairi da na assasa, mai girma gwamna ya dauki nauyin duk kuɗaɗen Alluna da Satifiket da Tufafi da sauran kayan da ɗalibai suka saya zai biya za mu mayar musu da kuɗin da suka kashe”.
You must be logged in to post a comment Login