Labarai
Gwamna Yahaya Bello, ya tsallake rijiya da baya
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya tsallake rijiya da baya bayan wasu ‘yan bindiga sun buɗe wa ayarin motocinsa wuta a kan hanyarsa ta zuwa Abuja.
Wata sanarwar da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar ta ce maharan sun kai wa tawagar gwamnan harin ne sanye da kakin sojojin.
Kafofin yaɗa labarai da dama sun rawaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa ziyarar aiki daga babbaban birnin Jiahar Lokoja.
You must be logged in to post a comment Login