Labarai
Gwamna Zulum yaƙi amincewa a sanya sunansa a rukunin ɗakunan kwanan ɗalibai
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi watsi da sanya sunansa a wasu rukunin gidajen kwanan ɗalibai guda biyu domin karrama shi.
Rukunin gidajen wanda suke a kwalejin kimiyya da fasaha ta Ramat da ke Maiduguri, mallakin gwamnatin jihar.
Zulum yaƙi amincewar ne a ranar Litinin lokacin bikin ƙaddamar da dakunan kwanan guda 1,500, wanda ma’aikatar ilimi da fasaha da kirkire-kirkire ta jihar ta gyara.
Tunda fari dai an sanya wa tagwayen aikin suna “Injiniya Farfesa Babagana Umara Zulum male students hostel” amma gwamnan ya ƙi amincewa da hakan.
A cewar Zulum “A’a ba zan bari a sanya sunana a duk wani aiki ba da aka gudanar a zamanin da nake kan karagar mulki kamata ya yi a bari sai bayan na bar mulki”.
Gwamna Zulum ya yabawa kwamishinan ilimi mai zurfi a fannin kimiyya, da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire, Injiniya Dr. Babagana Mallambe Mustapha, bisa ga irin rawar da ya taka wajen ciyar da kwalejin gaba.
You must be logged in to post a comment Login