ilimi
Zulum ya dakatar da hukumar gudanarwar kwalejin fasaha ta Ramat
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/09/Borno-school-school.jpg)
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin hukumar gudanarwar kwalejin kimiyya ta Ramat da ke jihar na tsawon watanni shida.
Gwamnan a wata ziyarar ba-zata da ya kai a ranar Talata ya kadu da ganin yadda dakunan gwaje –gwajen kwalejin suka daina aiki.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan jihar Malam Isa Gusau ya fitar.
A cewar sanarwar, gwamnan ya ziyarci kwalejin kimiyya da misalin karfe 9:00 na safe inda ya ga yawancin dakunan gwaje -gwajen ba sa amfani, inda wasu ke rufe har sun yi yanar gizo -gizo da beraye saboda rashin kulawa.
Idan za a iya tunawa Zulum tshohon dalibin kwalejin kimiyyar ne daga 1986 zuwa 1988 kuma ya taɓa rike mukamin shugaban kwalejin daga 2011 zuwa 2015.
.
You must be logged in to post a comment Login