Labarai
Gwamnan Bauchi ya ƙara ƙirƙiri sabbin masarautu

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya tabbatar da karin masarautun gargajiya a jihar.
Gwamna Bala ya sanar da hakan ne bayan da kwamitin kirkiro sabbin masarautu ya mika masa rahotonsa, wanda ya yi nazari kan samar da masarautu masu daraja ta biyu guda 13 da masu daraja ta uku guda biyu da kuma karin hakimai 111.
Da ya ke jawabi bayan kammala sanar da tabbatar da karin masarautun, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ce, gwamnatinsa ta yi hakan ne domin bai wa yankuna da dama cin gashin kansu da kuma ba su damar kawo ci gaba ga mutanen su.
You must be logged in to post a comment Login