Kaduna
Gwamnan Jahar Kaduna yace Jahar ta ginu ne akan zaman lafiya da tabbatar da adalci.

Gwamnan jahar kaduna Malam Uba Sani yace jahar ta ginu ne akan zaman lafiya da tabbatar da adalci a kasar nan dama nahiyar Afrika .
Gwamnan yace yace zaman lafiya jahar babban misali ne wanda za ayi amfani da shi a dauka kacin fadin kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a zagayowar ranar bikin zaman lafiya na duniya na wannan shekarar da aka gudanar a jahar.
Gwamnan wanda Kwamishinan tsaron cikin gida Sule Shu’aibu ya wakilce shi, yace taken taron na bana tunatarwa ce da daukar matakin gaggawa, don karfafa zaman lafiya a jahar.
You must be logged in to post a comment Login