Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kabilar Igbo ba zasu iya shugabantar Najeriya su kadai ba- Rochas Okorocha.

Published

on

Tsohon Gwamnan jahar Imo kuma dan majalisar dattijai Sanata Rochas Owelle Anayo Okorocha, ya bayyana cewa kabilar Igbo ba zai yiwu su sami shugabancin Najeriya su kadai ba, har sai sun hada kai da sauran kabilun Najeriya.

Sanata Rochas Okorocha ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a nan Kano bayan halattar wani daurin aure da yayi a fadar mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

Rochas Okorocha yace babu wani abu da zaka kira da suna shugabancin kabilar Igbo sai dai shugaban Najeriya da ya fito daga kabilar Igbo.

Sanata Okorocha yace kudu maso gabashin Najeriya a cikin tsarin tarayyara Najeriya yake, saboda haka babu wani dan asalin kabilar Igbo da zai zama shugaban Najeriya har sai ya samu goyon bayan sassan kasar nan.

Ya kara da cewa  hakan yana da amfani kwarai da gaske wajen ganin Najeriya ta dinke a matsayin kasa daya.

Sannan tsohon gwamnan na jahar Imo yace ya zo Kano ne domin ya ga abokinsa kuma gwamnan jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje .

Rochas Okorocha ya koka da rikicin da yake faruwa a jam’iyyar  APC tsakanin shugaban ta na kasa Adams oshiomole tare da gwamnan jahar Edo  Godwin Obaseki wanda yace hakan na iya jawo wa jam’iyyar matsalar faduwa zabe a zaben shekarar 2023.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!