Labarai
Gwamnan Jigawa ya sha al’washin bibiyar banun nan na Walida

Gwamnatin Jigawa ta ɗauki alwashin ci gaba da bibiyar harkokin da suka shafi Walida har zuwa ƙarshe domin tabbatar da adalci.
Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da iyayen Walida da lauyansu a gidan gwamnatin jihar, inda ya musu alƙawarin cewa zai tabbatar an yi wa ƴarsu adalcin da ta cancanta.
Ana dai zargin wani jami’an tsaron farin kaya na DSS ne da safarar Walida Abdulhadi, inda ta zauna a wajen shi, har ya haihu masa a Abuja.
“Yanzu haka Walida tana ƙarƙashin kulawarmu, ana duba ta domin gyara mata tunani. Daga baya za mu mayar da ita wajen iyayenta.”
Gwamnan ya ƙara da cewa za su taimaka wa Walida da iyayenta da tallafi domin inganta musu rayuwa, “sannan za mu mayar da Walida makaranta mu ɗauki nauyinta domin ta samu ilimi mai kyau.”
Da yake bayyana abin da ya faru a matsayin ‘safara’ gwamna Namadi ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar an yi mata adalci ta hanyar bin hanyoyin doka da oda, “sannan duk wanda aka samu da hannu a lamarin dole zai fuskanci hukuncin da ya dace,” in ji shi.
A ƙarshe gwamnan ya nanata muradun gwamnatin jihar na kare ƴanci da martabar ƴan jihar Jigawa a duk inda suke a faɗin duniya.
Da yake bayani a madadin iyayen, lauyansu Barista Kabiru Adamu ya bayyana godiyarsa ga gwamna Namadi bisa sa baki da ya yi wajen ceto Walida.
You must be logged in to post a comment Login