Labarai
Gwamnan jihar Taraba zai fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Gwamnan jihar Taraba a tsakiyar Najeriya ya sanar da cewa zai fice daga jam’iyyar PDP mai adawa zuwa APC mai mulkin kasar a ranar Laraba mai zuwa.
Da yake magana yayin wata ziyara a filin wasa na Jolly Nyame ranar Asabar – inda nan ne wurin taron komawa APC din – Gwamna Agbu Kefas ya ce matakin komawa APC ɗin yana da alaƙa ne da ciyar da rayuwar mazauna Taraba, ba wai raɗin kansa ba.
Gwamnan na cikin waɗanda ba su halaraci babban taron PDP na ƙasa da aka gudanar a birnin Ibadan ba ranar Asabar, inda ta zaɓi sababbin shugabanni. Sauran su ne Gwamnan Rivers Fubara da Adeleke na jihar Osun.
Idan gwamnan ya fita daga jam’iyyar zai zama jihohin da PDP ke mulki sun koma takwas kenan, yayin da a baya-bayan nan gwamnonin Bayelsa da Delta suka koma APC ta Shugaba Tinubu mai mulki.
You must be logged in to post a comment Login