Labarai
Gwamnan Kano ya Kara nada kwamishinoni uku
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ƙara rantsar da sabbin kwamishinoni guda uku da majalisar dokokin jihar ta amince masa da ya naɗa su a matsayin sabbi.
Bayan rantsar da su ne, gwamnan ya buƙace sabbin kwamishinonin da su kasance masu yin aiki yadda ya kamata domin yiwa al’umma abin da ya dace.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau yayin rantsar da sabbin kwamishinonin a fadar gwamnatin Kano inda suka haɗar da Alhaji Ibrahim Ali Dala, Ibrahim Jibrin sai Hajiya Amina Abdullahi Sani.
Abba Kabir Yusuf ya kuma ce ‘an zaɓi sabbin kwamishinonin ne sabo da cancan da sa ran zasuyiwa al’umma aiki yadda ya kamata’.
An baiwa Hajiya Amina Abdullahi Sani ma’aikatar Ayyuka ta Musamman, Alhaji Ibrahim Namadi Dala Ma’aikatar Bibiyar aikin Gwamnati sai Alhaji Ibrahim Jibrin a matsayin shugaban Ma’aikatar kuɗaɗe.
Rahoton: Umar Abdullahi Sheka
You must be logged in to post a comment Login