Labarai
Gwamnan Kano ya taya al’umma Musulmai murnar zagayowar watan sallah ƙarama
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Yusuf ya mika sakon taya murna ga al’ummar Musulmi bisa samun nasarar kammala azumin watan Ramadan, tare da taya su murnar zagayowar watan ƙaramar Sallah.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin kyawawan ɗabi’u na tausayi, karamci, da’a, kishin kasa, da zaman tare da juna da aka sanya a cikin watan Ramadan.
Ya bukaci al’ummar Kano da su kasance masu roƙon Ubangiji da ya basu shugabanni na gari a duk jagorancin su na rayuwa.
Gwamna Yusuf ya yi wa al’ummar Kano alkawarin cewa gwamnatinsa za ta samar da ingantattun tsare-tsare don samar da zaman lafiya da hadin kai ga kowa da kowa.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya roki al’ummar Kano da su kasance masu wanzar da zaman lafiya domin ci gaban Kano da ƙasa baki daya.
Ya kuma ba da shawarar a guji tukin ganganci a lokacin bikin Sallah da sauran abubuwan da basu da ce ba domin tabbatar da tsaron al’umma.
Gwamnan ya mika sakon taya murna ga daukacin al’ummar musulmi da sauran al’ummar Kano da za su gudanar da bukukuwan karamar Sallah.
You must be logged in to post a comment Login