Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano ya yi barazanar tsige jami’an Gwamnati masu saba wa manufofin sa

Published

on

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce duk wani Kwamishina ko mai ba shi shawara da ya san ba zai iya gudanar da manufofin gwamnatin sa yadda ya kamata ba, ko kuma yana da wata manufa ta daban da za ta kawo tsaiko ga ci gaban gwamnati, to ya gaggauta a jiye muƙaminsa kafin gwamnati ta ɗauki matakin cire shi.

 

A cewar gwamnan, gwamnatin sa ta zo ne domin samar da ingantaccen shugabanci da kuma kawo sauyi mai amfani ga al’ummar jihar Kano, saboda haka ba za ta bari wasu mutane su yi amfani da muƙamansu wajen kawo ruɗani ko hana aiwatar da manufofin gwamnati ba.

Gwamnan ya kuma gargadi duk wani jami’in gwamnati da ke nuna halin ko-in-kula wajen gudanar da aikinsa da cewa gwamnati za ta ɗauki mataki mai tsauri a kansa, domin al’ummar jihar Kano sun ba su amanar jagoranci ne domin yi musu aiki yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!