Connect with us

Labarai

Cire tallafin mai ya ceci Najeriya daga fadawa matsalar tattalin arziƙi – Tinubu

Published

on

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na cire tallafin man fetur ya ceci Najeriya daga fadawa cikin matsananciyar matsalar tattalin arziƙi, tare da shimfiɗa tubalin farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi bakuncin wasu gwamnoni da suka kai masa ziyarar taya murnar bikin babbar Sallah da kuma cika shekara uku da hawansa mulki.

 

Ya ce duk da cewa cire tallafin ya jawo wa ‘yan Najeriya ƙalubale da raɗaɗi, matakin ya zama dole domin ceto ƙasar daga durƙushewar kuɗaɗenta da kuma dawo da daidaito a tattalin arziki.

 

Tinubu ya ce “tsawon shekaru Najeriya na kashe kuɗaɗe masu yawa wajen biyan tallafin man fetur wanda a cewarsa ya fi amfanar kaɗan daga cikin jama’a, yayin da muhimman fannoni kamar noma da ababen more rayuwa suka rasa jarin da suke buƙata. ”

 

Ya ƙara da cewa “tattalin arzikin ƙasar na nuna alamun farfaɗowa, inda noma da ayyukan gine-gine ke ci gaba da bunƙasa.”

 

Shugaban ya kuma yaba wa gwamnonin jihohi bisa haɗin kai da goyon bayan da suka ba gwamnatinsa wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

 

Ya ce “a yanzu jihohi ba sa fama da matsalar neman tallafi daga gwamnatin tarayya domin biyan albashi kamar yadda aka saba a baya.”

 

A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yaba wa jajircewar Tinubu wajen tinkarar matsalolin da ke tattare da tallafin mai, yana mai cewa shugaba ya nuna ƙarfin hali wajen ɗaukar matakan gyaran tattalin arzikin ƙasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!