Connect with us

Labarai

Zan rage matsalar cin hanci idan na zama shugaban Najeriya – Peter Obi

Published

on

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin rage cin hanci da rashawa da kuma tsadar tafiyar da gwamnati idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027. 

 

Obi ya bayyana hakan ne bayan samun tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban taronta da aka gudanar a Abuja, inda ya ce za a karkatar da kuɗaɗen da ake ɓarnatarwa zuwa muhimman fannoni na tattalin arziki.

Ya kuma jaddada muhimmancin bin doka da oda, yana mai cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cikakken ‘yancin bangaren shari’a ba tare da tsoma bakin gwamnati ba. A cewarsa, hakan zai taimaka wajen jawo masu zuba jari da kuma ƙarfafa amincewar jama’a da cibiyoyin gwamnati.

Baya ga haka, Obi ya zargi gwamnatin da ke mulki da takura wa jam’iyyun adawa, yana mai cewa wasu na fuskantar tsangwama da hana gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci. 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!