Labarai
Gwamnan Katsina ya jagoranci tawagar haduwa da takwarorinsu na Kasar Nijar
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya jagoranci wata tawagar Gwamnoni don haduwa da takwarorin su na kasar jamhuriyar Niger a a garin Maradi a wani mataki na yunkurin dakile ayyukan ta’addanci a kan iyakokin kasar nan.
Gwamnonin sun hada da Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle da takwaransa na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da kuma na jihar Kebbi Atiku Bagudu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran Gwamna Aminu Bello Masari, Abdu Labaran, inda ya ce wannan wani mataki ne na dakile ayyukan ta’addanci da suke damun yankunan su.
Sanarwar ta kuma bayyana Kananan hukumomin da ayyukan ‘yan ta’addar su ka shafa da cewa, sun hada da: Dandume da Sabuwa da Faskari da Kankara da Dan-Musa da Safana da Batsari da kuma Jibiya, wadanda kananan hukumomin ne da suke makotaka da dajin Rugu da ya kaskance maboyar ‘yan ta’adda.
Ta cikin sanarwar dai gwamna Aminu Bello Masari, ya kara da cewa, wasu bangare na jihar Maradi na daya daga cikin hanyoyin da ‘yan ta’addar ke amfani dasu wajen shigo da muggan makamai.
Wannan na zuwa ne a yayin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya sanya hannu kan yarjejeniyar aiki da jami’an tsaro da sauran Gwamnoni dake makotaka da jihar.