Coronavirus
Gwamnan Katsina ya rufe Daura domin dakile yaduwar Coronavirus
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya rufe garin Daura domin dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin Daura.
Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da manema labarai cewar rufewar za ta fara aiki ne da karfe bakwai na safiyar ranar Asabar bayan.
A cikin gwajin kwayar cutar Covid-19 na mutane 23 da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa ta yi a Abuja, ya nuna cewa mutane 3 daga cikin sun a dauke da kwayar cutar ta Coronavirus kuma dukannin su ‘yan uwan likitan da ya kamu da cutar har ya rasa ransa ciki harda ‘ya’yan sa guda biyu da su ka kamu da cutar a yanzu haka.
Masari ya ce “Mun tattauna da jami’an tsaro da kwamitin karta kwana game da cutar karkashin mataimakin gwamna da kuma masu ruwa da tsaki inda mu ka yanke shawara rufe Daura domin gudun yada cutar ta Covid-19 a cikin al’umma, mun barwa jami’an tsaro su kula sosai yayin wannan dokar, sannan duk wata karamar hukumar da a ka samu da bullar cutar ita ma za a rufe ta. A don haka al’umma da su bada hadin kai cewa sun zauna a cikin gidajen su”. A cewar sa.
Sai dai kuma ya tabbatar da cewar rufewar ba za ta shafi wasu wuraren bayar da magani uku mallakar gwamnati guda uku da sauran su tare da kantunan shiyar da kayan masarufi
You must be logged in to post a comment Login