Connect with us

Coronavirus

Ma’aikatan lafiya 14 sun kamu da Corona a Katsina

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta ce an samu ma’aikatan lafiya 14 da suka kamu da cutar Covid-19 a jihar.

Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari shi ne ya bayyana hakan yayin wata ganawarsa da manema labarai.

Gwamna Masari ya ce jami’an lafiya 10 da suka kamu da cutar suna aiki ne a asibitin gwamnatin jihar.
Likitoci 4 kuma daga asibitoci masu zaman kansu.

Wakilinmu a jihar Katsina Abdullahi Garba Jani ya rawaito mana cewa Gwamna Masari ya ce Likitocin sun samu cutar ne a yayin ayyukansu na ceton rayukan al’umma a asibiti ba tare da sun san cewa mutane dake zuwa gunsu na dauke da cutar Covid-19 ba.

Karin labarai:

Gwamnan Katsina ya rufe Daura domin dakile yaduwar Coronavirus

Za a rufe Katsina ba shiga ba fita daga Talata

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!