Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Ma’aikatan lafiya sun kamu da Corona a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da shigar Cutar Coronavirus cikin ma’aikatan lafiya a wasu asibitoci biyu dake jihar.

Kwaminshinan lafiya na jihar kuma shugaban kwamaaitin dakile yaduwar cutar ta Covid-19 a jihar, Dr. Abba Umar ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Dr. Abba ya ce asibitocin da abin ya faru sun hada asibitin Rashid Shakoni dake Dutse sai kuma asibitin gwamnatin tarayya dake Birnin Kudu (FMC-BKD).

Dr. Abba ya kara da cewa na Rashid Shakoni din sun dauki cutarne a wurin wata mai juna biyu da aka kawota daga karamar hukumar Miga wadda bayan ‘yan kwanaki ana bata kulawa, alamu suka nuna tana dauke da cutar Covid-19 kamar yadda sakamakon gwajin da aka yi mata ya nuna wadda itace mutum na biyu da ta rasu sanadiyyar cutar a Jigawa.

Karin Labarai:

Ma’aikatan jinya 18 sun kamu da Corona a Kano

Ma’aikatan lafiya 14 sun kamu da Corona a Katsina

Ma’aikatan lafiya 7 sun kamu da Coronavirus a Borno

Haka abin yake a asibitin Tarayya na Binin Kudu can ma dai wani marar lafiyane ya kwanta, wadda daga karshe shima aka gwadashi ya kamu da cutar.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito kwaminshinan na cewa tuni dukkan likitoci da jami’an lafiyar da suka kula da wadancan mutane an killacesu kuma harma an gano wasu daga ciki sun kamu da cutar, duk da har kawo yanzu yace basu gama kididdige ko jami’an lafiya nawa ne cutar ta shafa fa.

Wannan dai na zuwa ne yayinda ake ta samun rahotonnin jami’an lafiya dake kamuwa da cutar ta Covid-19 a sassa daban-daban na kasarnan.

A makociyar jihar Jigawan wato Kano kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar ta tabbatarwa da Freedom Radio cewa Likitoci 34 ne suka kamu da cutar a jihar zuwa makon da muke ciki.

Haka abin yake inda suma ma’aikatan jinya da unguzoma 18 suka kamu da cutar a jihar Kanon.

Ita ma jihar Katsina dake makotaka da jihar Jigawan gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa wasu jami’an lafiya a jihar sun kamu da cutar ta Covid-19.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!