Connect with us

Labarai

Gwamnan Sokoto ya gargadi masu adawa da su dena siyasantar da matsalar tsaro

Published

on

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya gargaɗi ƴan hamayya da sauran ƴan jihar da su guji sanya siyasa a cikin matsalar tsaro, inda ya nanata cewa hakan na ƙara ta’azzara matsalar a jihar.

 

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ƙaramar hukumar Silame a ci gaba zagayen ziyarce-ziyarcen jaje a wuraren da ƴanbindiga suka kai hare-haren a ƴan tsakankanin nan.

 

Gwaman  ya ce matsalar tsaro al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, don haka ya kamata a riƙa bi a hankali a duk lokacin da ake magana game da tsaro,” in ji shi kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya bayyana.

 

Ya ce gwamnati ba za ta lamunci yadda wasu suke fakewa da sunan siyasa ko tattauna al’amuran yau da kullum ba suna kawo tsaiko a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da tsaro a jihar ta Sokoto.

 

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro ba dare ba rana domin samar da tsaro, inda ya ce an fara ganin sakamakon ƙoƙarinsu.

 

Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda wasu suke taimako ƴanbindiga ta hanyar ba su bayanai, inda ya ce akwai buƙatar al’umma su taimaka wa gwamnati ta hanyar ba jami’an tsaro bayanai masu muhimmanci kan harkokin ƴanbindiga.

 

A ziyarar, gwamna Aliyu ya ba iyalan duk wanda aka kashe naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, inda jimilla ya raba naira miliyan 66 da buhun shinkafa 165 a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!