Ra'ayoyi
Gwamnati bata kyautawa ƴan ASUU ba – Bulama Bukarti
Daga shafin Audu Bulama Bukarti
Gaskiya Fedaral Gamman ba ta kyauta ba da ta biya ƴan ASUU rabin albashin watan Oktoba maimakon ta biya su duka.
Duk da cewa sai ranar 14 ga watan suka janye aiki, kamata yayi kawai a biya su watan gaba ɗaya, musamman ma tunda buƙatun da suka sa aka yi yajin aikin ma basu biya ba. Sam ba dace a haɗa mari da tsinka jaka ba.
Amma na ji ance ASUU za ta yi taro ranar Litinin domin duba yiwuwar komawa yajin aiki.
Ina fatan shugabannin ASUU za su kai zuciya nesa, su kuma yi aiki da hankali.
Su lura cewa yajin aikin watanni takwas baya din da suka yi ma bai amfane su da komai.
Saboda haka, idan suka koma yajin aiki, gidan jiya kawai za a koma.
Sabon yajin aiki kawai zai ƙara kawo tsaiko ne ga karatun ƙannenmu kuma ya ƙara jefa mambobin ASUU cikin ƙangi wahala.
Labarai masu alaka:
Kamar yadda hirarsa ta kwanan nan ta ƙara fito da abin fili, Buhari fa ba shi da tausayi, bai san ya kamata ba kuma matsalar talaka ba ta dame shi ba.
Don haka, idan ma ASUU ta koma yajin aiki, wallahi ko a kwalar Buhari.
Maimakon tsunduma cikin wani yajin aikin, gara ASUU ta ci gaba da tattaunawa da Gwamnati kuma su ci gaba da matsa mata ta kafafen yaɗa labarai da na sada zumunta tun da ba za su iya zanga-zanga ba.
Idan suka ɗau wannan hanya, duka za mu fito mu taya su wannan yaƙin.
Daga ƙarshe, ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta biyan ƴan ASUU sauran albashin watan Oktoba.
You must be logged in to post a comment Login