ilimi
Gwamnati ta gaza saurarar mu muna dab da fara yajin aiki- ASUU
Kungiyar Malaman Jami’oin kasar nan ASUU ta ce kwanaki biyu da karewar wa’adin data bawa gwamnatin tarayya na tafiya yajin aikin data kuduriyi, idan bata biya mata bukatun ta ba.
A cewarta ta har zuwa yanzu gwamnatin tarayya bata tuntubeta ba kan ikirarin da ta yi
Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan jiya yayin da yake zantawa da jaridar Vanguard.
Emmanuel Osodeke ya ce a domin haka kungiyar na gab da daukan mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login