Labarai
Gwamnati zata kashe miliyan 600 don gyara kasuwar Dawanau
Hukumar bunkasa harkar noma ta jihar Kano (KSADP), ta ce ‘za ta kashe kimanin Naira miliyan 600 domin gudanar da ayyukan inganta kasuwar hatsi ta kasa da kasa ta Dawanau.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwararre a fannin kula da ayyuka na hukumar Malam Ameen Yassar ya fitar a ranar Laraba,
Yassar ya ce, Bankin ci gaban Musulunci (ISDB) tare da hadin guiwar Asusun inganta jin dadin rayuwa (lives and livelihood funds) ne suka dauki nauyin shirin.
Ya ce, ayyukan da za a gudanar, sun hadar da titi mai nisan kilomita hudu, magudanar ruwa da fitulun kan titi, inda ya ce, ‘an bayar da wannan kwangilar ne ga kamfanin Labour Technical Services Ltd, kan kudi Naira miliyan 508.
Yassar ya kara da cewa, an baiwa kamfanin AITEC Infraconsult Ltd kwangilar gina gidan wanki guda uku da masallaci da ofishin ‘yansanda da ofisoshi da dakin taro, a kan kudi naira miliyan 92.Wanda ake aa ran gama aikin cikin watanni 12.
You must be logged in to post a comment Login