Labaran Kano
Gwamnatin Kano za ta magance fashewar bututun ruwa
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jihar na daya daga cikin manyan ayyuka da za ta fi ba da fifiko a shekara mai zuwa.
Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano Sadiq Aminu Wali ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala kare kunshin kasafin kudin ma’aikatar gaban kwamitin kula da albarkatun ruwa na majalisar dokokin Kano a jiya litinin.
Ya ce, ma’aikatar za ta zage dantse wajen bullo da shirye-shirye wadanda za su taimaka gaya wajen magance matsalolin da ake fuskanta a bangaren samar da ruwan sha ga al’ummar jihar.
A nasa bangaren shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano Injinya Garba Ahmed Kofar Wambai, ya yi kira ga al’ummar Kano da su rika sanar da hukumar akan lokaci a duk lokacin da suka samu fashewar bututuwan ruwa a yankunansu.
Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito shugaban hukumar WRECA Injinya na cewa hukumar za ta saya sabbin motoci na zamani domin fsukantar kalubalen da ke gabanta.