Connect with us

Labarai

Karuwar jama’a shike kawo matsalar ruwan sha a Kano

Published

on

Hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano tace  matsalolin ruwan sha da ake fuskanta a yanzu a jihar Kano nada nasaba da karuwar jama’a a birnin na Kano.

Daraktan mulki na Hukumar Injiniya Musbahu Nasir ne ya bayyana haka a cikin shirin Duniyar mu a yau na nan Freedom Radio.

Injiniya Musbahu yace kwararowar wasu al’ummar zuwa jihar Kano na da nasaba da karancin ruwan

Mazauna Tokarawa sun yi kururuwar neman dauki

Al’ummar Dakata sun koka akan ginin shaguna bisa magudanar ruwa

Shi kuwa Injiniya Magaji Hussain cewa yayi har yanzu akwai bukatar karin wasu sababbin matatun ruwa a Kano kasancewar yawan mutane a Kano yana karuwa wanda hakan yasa jama’a ke cigaba da kara tsananin bukatar ruwan a yanzu.

A nasa bangaren shugaban hukumar samar da ruwan sha ta Jihar Kano yace matsalar ruwan sha da ake faman cece kuce akai a Kano musamman a kwaryar birnin  na da alaka da rashin hakuri  da kuma yadda wasu ke Siyasantar da al’amarin.

Bakin sunyi kira ga al’ummar Kano dasu kara hakuri domin kuwa nan da shekaru shida masu zuwa matsalar rashin ruwan sha a Kano za tazo karshe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!