Labarai
Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Lamurde

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar hana fita ta awanni 24 a ƙaramar hukumar Lamurde sakamakon sake barkewar rikicin ƙabilanci a wasu sassan yankin.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Humeashi Wonosikou, ya fitar, gwamnatin jihar ta bayyana rikicin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tare da umartar jami’an tsaro su tabbatar da bin dokar hana fitan domin dawo da doka da oda.
An kuma buƙaci mazauna yankin su bi dokar tare da bai wa jami’an tsaro bayanai da za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya, yayin da gwamnan ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rikicin dai ya samo asali ne daga arangama tsakanin al’ummomin Chobo community da Bachama community, inda rahotanni suka ce aƙalla mutane biyu sun rasa rayukansu kafin a ayyana dokar hana fitan, yayin da ’yan sanda ke ci gaba da tattara cikakken bayani kan asarar rayuka.
You must be logged in to post a comment Login