Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Ganduje ta ɗauki masu bukata ta musamman aiki

Published

on

A yau Laraba ne mutane masu bukata ta musamman su tara za su karbi takardun kama aiki a matakin gwamnatin jihar Kano.

Tun da fari dai, masu bukata ta musamman su 134 ne suka nemi aiki a matakai daban-daban a nan Kano.

Sai dai a zantawar da wakilinmu Mukhtar Iliyasu Dumbulun ya yi da babban mai taimakawa gwamnan jihar Kano kan harkokin mutane masu bukata ta musamman Tasi’u Shehu Garko ya sanar da cewa, yanzu haka mutum tara ne suka hallara a ofishin shugaban ma’aikata domin karbar takardar kama aikin.

Haka kuma, Ya ce, sauran ragowar mutane masu bukata ta musamman din da suka nemi aikin za a tattauna yadda za a ba su takaradun kama aikin a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!