Labarai
Gwamnatin Ganduje za ta bada zakkar Naira Miliyan 30
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin bayar da Naira Miliyan talatin ga hukumar Zakka da Hubusi ta jihar domin raba wa mutanen da suka cancanta.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da rabon Zakkar naira Miliyan goma da Alhaji Aminu Alhasan Dantata, ya bai wa hukumar Zakka da Hubusi oan raba wa ga mutane fiye da dari takwas da aka gudanar a dakin taron na Correnation da ke gidan gwamnati.
Ganduje ya kuma ce, gwamnati ta kammala ginin sabon ofishin hukumar Zakka na din-din-din don gudanar da harkokin hukumar.
A nasa jawabin shugaban hukumar Zakka ta jihar Kano Malam Ibrahim Muazzam Mai bushira, ya ce, kamata ya yi masu bayar da Zakka da mawadata su kai Zakkar su hukumar don tabbatar da ganin ta je ga mabukata.
Wadanda aka raba wa Zakkar a yau, sun hadar da maza da mata cikin su har da masu bukata ta musamman.
Rahoton: Abba Isah Muahammad
You must be logged in to post a comment Login