Manyan Labarai
Gwamnatin jahar Kaduna ta bukaci a kau da Almajiranci
Kwamishiniyar cigaban alumma ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba tayi kira ga jihohin Arewacin kasar nan sha tara 19 da su samar da manufofi da tsare-tsare mai kyau wajen cimma nasarorin kauda karatun Almajiranci a yankin.
Hajiya Hafsat Baba tayi wannan kiran ne yayin da take kare kunshin kasafin kudin ma’aikatar ta ,a gaban kwamitin kula da bunkasa al’umma na majalisar dokoki ta jihar.
Kwamishiniyar ta nunar cewar, kafin a kauda Almajirai akan tituna kamata yayi a samar da tsare-tsaren da suka dace wajen shawo kan matsalar.
“Ta ce nauyin ya rataya a wuyan dukkanin jihohin Arewacin kasar nan sha tara 19 ta yadda za su samar da manufofi da za su warware matsalar acewar Hajiya Hafsat “
Har ‘ila yau Kwamishiniyar ta ce almajiran da ma’aikatar ta kawar akan titinan jihar ta Kaduna sun gano cewar sun fito ne daga jihohin Arewacin kasar nan suka fito.