Labarai
Gwamnatin Jigawa ta amince da kudirin tilasta yin gwajin ga masu shirin yin Aure

Majalisar zartaswar jihar Jigawa, ta amince da kudirin tilasta yin gwajin kwayoyin halitta ga mutanen da ke shirin yin Aure.
Da ya ke yi wa manema labarai karin haske game da zaman majalisar da ya gudana karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar ta Jigawa Injiniya Aminu Usman Gumel a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse, Sakataren yada labaran gwamnan Malam Hamisu Muhd Gumel, ya ce, an dauki matakin ne domin rage yawan haifar yara masu dauke da cutuka.
Haka kuma, Malam Hamisu Muhd Gumel, ya kara da cewa, majalisar zartaswar ta sake amincewa da bukatar kashe sama da Naira miliyan 300 domn gina wasu cibiyoyin samar da Ruwan sha a sassan jihar.
You must be logged in to post a comment Login