Jigawa
Gwamnatin Jigawa ta ja kunnen Yan Kwangila

Ma’aikatar samar da wutar lantaki da makashi ta jihar Jigawa ta ce bazata lamunci yin aiki ba bisa ka’ida ba ga dukkanin dan kwangilar dake aiki a ma’aikatar.
Kwamashinan ma’aikatar Injiniya Dakta Surajo A. Musa, wanda ya samu wakilcin daraktan samar da fitulu masu amfani da hasken rana na ma’aikar injiniya Akilu Jafaru Badakaya, ne ya bayyana haka yayin tallata ayyukan kwangila na samar fitulu masu amfani da hasken rana na ayyukan mazabun ‘yan majalisu 30 da ke jihar.
Ya ce aikin samar da fitulun zai lakume kudi sama da naira miliyan dubu 887.
A nasa jawabin babban daraktan hukumar lura da ingancin ayyuka na jihar Jigawa wanda ya samu wakilcin injiniya Danazumi Musa, yace kamar yanda tsarin hukumar yake zasu cigaba sanya idanu tare da hadin gwiwa da kungiyoyi domin tabbatar da ingancin ayyukan da za’a gudanar.
You must be logged in to post a comment Login