Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da shirin Allurar Rigakafin cutar Amai da Gudawa

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi, ta kaddamar da shirin Allurar Rigakafin cutar Amai da Gudawa na Cholera don kaucewa barkewar annobar a jihar.

Gwamnan jihar Bala Mohammed, ne ya kaddamar da shirin a ranar 28 ga watan Yuli a babban birnin jihar na Bauchi.

Yace shirin na Rigakafin wanda ake durawa ta baki za’ayi shi ga al’ummar jihar kyauta, a yunkurin samarwa da al’umma ingantacciyar lafiya.

Gwamnan ya kuma ce, za a yi aiki kafada-da-kafada da gwamnatin tarayya wajen samar da wadatatun kayan aikin lafiya.

Ya kuma bukaci malaman adddini da shugabannin al’umma da su cigaba da wayar da kan al’ummar jihar don kare kan su da kuma karbar rigakafin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!