Labarai
Gwamnatin Jigawa ta Kaddamar da fara aikin Hanya me tsawon Kilo mita 30 da za ta lakume kimanin Naira Biliyan 7

Gwamnatin jihar Jigawa ta Kaddamar da fara aikin Hanya me tsawon Kilo mita 30 da ake sa ran aikin zai lakume kimanin Naira Biliyan 7.
Gwamnan Jihar ta Bakin Kwamishinan ma’aikatar ayyuka da Sufuri na jihar ne ya bayyana hakan yayin Kaddamar da fara aikin da ya tashi daga Garin Tsakuwawa, Koya zuwa Kafin Hausa a karamar hukumar Miga ta jihar Jigawa.
Yana Mai cewar, aikin titin yana daya daga Cikin Manyan ayyukan da Gwamnatin Jigawa ta yi a Cikin shekaru biyu da hawa Mulkin Jihar
Daga Cikin mutanen da suka halarci Kaddamar da fara aikin sun hadar da Kakakin Majalisar dokokin jihar Jigawa, da Kuma Dan Majalisar dokokin jihar Mai wakiltar karamar hukumar Miga Alhaji Haruna Aliyu Dan Gyatim da Sauran Kwamishinoni da ‘yan Majalisu na Jiha dana Tarayya
You must be logged in to post a comment Login