Kasuwanci
Gwamnatin jihar Kano zata bada hayar Kadada 1,000 don noman Kasuwanci
Gwamnatin jihar Kano , ta amince da bada hayar kadada 1,000 ga manoma ‘yan kasuwa don Noman abincin dabbobi wadatacce karkashin shirin bunkasa Noma da kiwo na jiha wato Kano state Agro Pastoral Development Project,KSDAP , da bankin musulunci ke daukar nauyin shirin.
Filayen da za’a bayar hayar an zabo su ne a curare daban -daban cikin kananan hukumomi 16 dake cikin jiha.
Shugaban shirin na jiha Malam Ibrahim Garba Muhammad Gama, ne ya bayyana haka jim kadan bayan ganawar sa da tawagar gwamnatin jiha , karkashin Babban Sakatare na ma’aikatar gona ta jiha Alhaji Adamu Abdu Faragai.
Malam Ibrahim Garba , ya tabbatar da cewar gwamnati ta amince da tsarin wanda zai samar da manoma masu zaman kansu da zasu yi Noman kasuwanci mai yawa da zai samar da abincin dabbobi.
Labarai masu alaka.
Gwamnatin Kano zata zaunar da makiyaya guri daya
Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi
Wanda kawo yanzu haka shirin ya samu kamfani 20 masu saka hannun jari a bangaren noman da zasu noma filayen kadada 50, da zasu lura da yadda aiyyukan nomawa tare da girbewa da hada kayan tare da yadda za’a samar da hanyoyin cinikayya.
Hakan zai kara samar da wadataccen abincin dabbobin , samar da madarar Shanu tare da gudanar da bayen na Shanu.
A jawabin na shugaban kamar yadda takardar kakakin shirin Aminu Kabir Yassar , ya sakawa hannu ta ambata, tace Malam Ibrahim Muhammad Garba, ya ce tuni gwamnati karkashin ma’aikatar aikin noma ta amince da a ware tare da amfani da kadada 20, don habbaka noman ciyawar Shanu a gurin Kiwo na Dudduru dake karamar hukumar Ajingi.
Bugu da kari shirin ,ya tattauna yadda aikin gudanar da allurar rigakafi ta dabbobi tare da kafa Asibitin dabbobi da dakin gwaji a karamar hukumar Gwale , sai saka kayan aiki da bunkasa wajen bayen Shanu dake Kadawa a karamar hukumar Garun Malam , tare da bude sabon Asibitin dabbobi a garin Dansoshiya dake karamar hukumar Kiru.
You must be logged in to post a comment Login