Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Zamalek FC Dakata tayi bikin cika shekara 20

Published

on

Kungiyar Kwallon kafa ta Zamalek Fc, dake Dakata tayi bikin cika shekara 20 da Kafuwar Kungiyar.

Bikin wanda aka gudanar tare da fafata wasa a yammacin jiya Alhamis tsakanin tsofaffin ‘yan wasan kungiyar da wanda suke sabbin jini, a filin wasa na Sakandiren Kawaji dake unguwar Dakata an tashi wasan canjaras , 0-0 kowacce kungiya na nema.

Bayan tashi daga wasan da yake jawabi mai horar da kungiyar Ali Ibn Hassan, ya bayyana jin dadin sa tare da zayyano nasarorin da kungiyar ta samu a tsawon lokacin da ta shafe tun shekara ta 2000, kana ya ce abun ya zo masa dai -dai sakamakon yazo a gabar da yake murnar daurin auren sa.

Suma tsofaffin ‘yan wasan kungiyar sun bayyana jin dadin su ya yinda wanda suke wakiltar kungiyar a yanzu suka sha alwashin cigaba da daga darajar kungiyar don bunkasa ta.

Labarai masu Alaka.

‘yan wasan jihar Kano sun samu nasara a Ramat cup

Covid-19: An dakatar da kwallon kafa a Kano saboda Coronavirus

Shima jami’in gudanar da kungiyar kana mai lura da walwala yan wasa Malam Nura Bargo, ya yabawa ‘yan wasan tare da alakanta samun nasarorin kungiyar zuwa yanzu da da’ar ‘yan wasan da suka wakilce ta a lokuta daban -daban.

An karkare wasan na bikin muranar da karrama tsoffin yan wasan da suka wakilci kungiyar , da mai horar da kungiyar tare da ‘yan wasa masu da’a , da matasa masu wakiltar kungiyar a yanzu.

Dumbin ‘yan kallo ne suka shaida wasan , wanda aka yi amfani da wasu daga cikin matakan kare kai , na kamuwa daga Corona, na wanke hannu da saka Takunkumin hanci da Baki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!