Connect with us

Labaran Wasanni

Abia Warriors ta Nada Sabon Mai Horaswa

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors ta nada tsohon mataimakin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Imama Amapakabo a matsayin mai horas da kungiyar.

Imama Amapakabo, ya shafe tsawon lokaci ba tare da samun wani aiki ba bayan da ya rasa aikin mataimakin mai horas da kungiyar ta Super Eagles.

Manchester na neman tsawaita kwantaragi da Pogba

Ba dan wasan Najeriya cikin ‘yan wasa masu daraja a Afrika

Kungiyar ta Abia Warriors ta amince da Imama Amapakabo, wajen ci gaba da jan ragamar kungiyar har tsawon kakar wasanni biyu a yayin da suka kammala tattaunawa dashi a yau Alhamis.

Imama Amapakabo dai ya jagorancin kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers wajen lashe gasar Firimiya ta Najeriya karo na farko bayan shafe shekaru 32 ba tare da kungiyar ta lashe kofin ba.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,290 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!