Labarai
Gwamnatin jihar Lagos ta samar da kotuna 4 don sauraran kararrakin cin hanci da rashawa
Gwamnatin jihar Lagos ta samar da wasu kotuna guda hudu da zasu rika sauraron kararrakin cin hanci da rashawa da kuma laifukan cin zarafin bil’adam.
Babban jojin jihar Lagos mai shari’a Opeyemi Oke ne ya kaddamar da kotunan inda ya ce bude kotunan ya biyo bayan umarnin da babban jojin kasar nan justice Walter Onnoghen ga dukannin manyan joji na jihohin kasar nan da su samar da kotunan da zasu rika sauraron kararrakin da suka danganci cin hanci da rashawa.
Justice Oke ya bayyana cewa a yanzu haka akwai kimanin kararraki da suka shafi cin hanci da rashawa guda 500 gaban babbar kotun jihar Lagos wadanda zuwa yanzu an mika wasu zuwa sabbin kotunan.
Cikin wadanda suka halarci bikin kadammar da kotunan sun hadar da shugaban kotun kolin kasar nan Justice Zainab Bulkachuwa da da shugaban kotun daukaka kara dake zama a jihar Lagos Justice M.I Graba yayin da mataimakiyar gwamnan jihar Lagos Dr.Idiat Adebule ta wakilcin gwamnan jihar.
Sauran sun hadar da lauyan gwamnatin jihar Mrs Funmilola Odunlami wadda ta sami wakilcin Attorney Janar Mr.Adeniji Kazeem.